Ministocin Turai zasu gudanar da taro game da Girka
Ministocin Kudin Kasashen Turai zasu gudanar da wani taro a birnin Brussels, domin neman amincewa da matakin bayar da Tallafin kudi euro Miliyan 130 ga kasar Girka ko kuma kasar ta durkushe daga ranar 15 ga wata mai zuwa.
Wallafawa ranar:
Fira Ministan Girka, Lucas Papademos yana cikin wadanda zasu halarci taron tarr Ministan kudinsa domin ganin ya samu nasarar shawo kan Ministocin, yayin da Sakataren Baitulmalin Amurka Timothy Geithner yace suna lallashin Hukumar Bada lamini ta duniya don taimakawa Girka.
Ministan kudin kasar Faransa, Francois Baroin yace akwai yiyuwar tawagar Ministocin Turai zasu amince da Tallafin da zasu ba kasar Girka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu