Ministocin Turai sun sake gabatar da wasu sabbin matakai akan Girka
Ministocin kudi kasashen Turai sun sake gabatarwa kasar Girka sabbin matakai domin ceto darajar tattalin arzikinta, amma kungiyoyin kwadago a kasar Girka sun shirya gudanar da yajin aikin gama-gama domin nuna adawa da matakin tsuke bakin aljihun gwamnati.
Wallafawa ranar:
Jagoran tattaunawar Ministocin kudin kasashen turai yace sabbin matakan zasu hada da kudi euro biliyan 130 da za’a ba Girka domin ceto darajar tattalin arzikinta.
Jean-Claude Juncker yace ya zama dole 'Yan majalisun Girka su amince da matakan tsuke bakin aljihu a zamansu na ranar Lahadi.
Sai dai kungiyoyin kwadago a kasar Sun kira wani yajin aikin sa’o’I 48 da za’a fara a yau Juma’a domin nuna adawa da matakan tsuke bakin aljihun.
Mista Juncker, Fira ministan kasar Luxembourg yace akwai bukatar ‘yan siyasa a kasar Girka su bada tabbacin cim ma sabbin sauye sauye bayan kammala zaben da za’a yi a kasar a watan Afrilu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu