Isa ga babban shafi
EU-Girka

Kasashen Turai zasu sa ido ga harakokin kudin kasar Girka

Kungiyar Kasashen Turai ta bukaci sa ido kan harkokin kudin kasar Girka, domin tabbatar da cewa tana aiwatar da matakan tsuke bakin aljihun da aka sanya mata. Jami’in kungiyar, Jean Claude Juncker yace ya zama wajibi a ci gaba da sa ido kan harkokin kasar, duk da nasarorin da ta samu.

Babban Jami’in kungiyar Turai Jean-Claude Juncker  yana muhawara da Ministan kudin kasar Girka  Evangelos Venizelos a taron da aka gudanar a birnin  Bruxelles.
Babban Jami’in kungiyar Turai Jean-Claude Juncker yana muhawara da Ministan kudin kasar Girka Evangelos Venizelos a taron da aka gudanar a birnin Bruxelles. REUTERS/Yves Herman
Talla

Sai dai Ministan Kudin kasar Girka, Evangelos Vanizelos, ya yi zargin cewar, wasu daga cikin kasashen Turai basu bukatar kasar a cikin kungiyar Turai, saboda matsalolin da take fuskanta.

Ministan yace, wadannan kasashe suna wasa da wuta, inda ya kara da cewa, babu yadda za’ayi su fice daga cikin kungiyar.

Yanzu haka dai darajar Kudin euro ta fadi a kasuwar kasashen Asiya inda masu saka jari ke nuna fargaba game da yarjejeniyar da ba a cim ma ba tsakanin kasashen Turai da kasar Girka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.