Isa ga babban shafi
EU-Girka-IMF

Yunkurin Tallafawa kasar Girka ya gamu da Cikas

Yunkurin Tallafawa kasar Girka daga fita daga matsalar bashin da ke addabar kasar ya gamu da cikas, bayan da kasashen Turai suka jinkirta taron Ministocin kudi da zasu cim ma matsaya game da tallafin kudaden da zasu tallafawa Girka bayan kasa cim ma bukatunsu.

Masu zanga-zangar adawa da matakan Tsuke bakin aljihun gwamnati a kasar Girka.
Masu zanga-zangar adawa da matakan Tsuke bakin aljihun gwamnati a kasar Girka. REUTERS/John Kolesidis/Files
Talla

A yau Laraba ne Ministocin kudin kasashen Turai suka shirya gudanar da taro a Brussels game da Girka, amma daga bisani aka dage taron, kasancewar babu wani bayani a rubuce da suka samu daga Shugabannin Siyasar Girka wajen aiwatar da bukatun da aka gindaya wa kasar.

Fira Ministan kasar Luxembourg Jean-Claude Junker yace babu wani bayani da suka samu daga Shugabannin kasar Girka, game da yadda za’a aiwatar da tsare-tsaren tallafawa kasar da aka gabatar masu.

Fira ministan yace akwai wasu Karin yarjeniyoyi tsakanin kasar Girka da kungiyar kasashen Turai da kuma Asusun Bada tallafi na duniya IMF, tare da batun samar da kudin Euro Miliyan 325 da yadda za’a tabbatar da dorewar matakan biyan basukan da ke wuyan kasar.

Yace yau laraba tare da Ministocin Kudade na kasashen Turai zasu yi taro na musamman, inda zasu nazarci sauran batutuwan da ba a kammala warwarewa ba, yayin da a ranar Littini mai zuwa a sake wani zaman taron.

Kasar Girka dai na bukatar kudin da suka kai Euro Biliyan 230, domin warware matsalolin da ke wuyanta.

Sai dai al’ummar kasar na ci gaba da gudanar da zanga-zanga domin adawa da sabbin tsare tsaren tsuke bakin aljihun gwamnati da kasashen Turai da IMF suka bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.