Tattalin arzikin duniya kan iya shiga mawuyacin hali, inji Lagarde
Shugabar Hukumar Bada Lamuni ta Duniya, Christine Largarde, ta ce tattalin arzikin duniya zai fada cikin mawuyacin hali, muddin kasar Amurka ta gaza kara adadin yawan bashin da take ci. Largard ta bayyana fatar ta na ganin Majalisa ta kara yawan bashin da Gwamnati za ta iya ci a wanan sabon wa’adi na biyu.
Wallafawa ranar:
“Idan ba’a warware matsalar da sauri ba ta hanyar da ya kamata, ba kamar yadda akayi a wancan lokaci ba, wato kara yawan adadin cin bashin, zai zama tashin hankali ga tattalin arzikin duniya. Ina fata dukkan bangarorin zasu hada kai da kuma sanya kishin kasa da kuma tattalin arzikin duniya a gaba.” Inji Lagarde.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu