Isa ga babban shafi

Hukumomi sun gaza biyan 'yan wasa mata kudadensu gabanin gasar cin kofin duniya

Shugaban hukumar kulada kwallon kafa ta duniya FIFA Gianni Infantino, ya ce babu tabbacin hukumomin kwallon kafar kasashe da suka sami gurbi a gasar lashe kofin duniya ta mata da za a fara a gobe Alhamis, da kasashen Australia da New Zealand za su dauki nauyi, za su iya kammala rabawa ‘yan wasansu kudaden da ya kamata a basu.

Babu tabbacin hukumomin kwallon kafar kasashe za su iya kammala rabawa ‘yan wasansu kudaden da ya kamata a basu kafin fara gasar lashe kofin duniya  ta mata a gobe.
Babu tabbacin hukumomin kwallon kafar kasashe za su iya kammala rabawa ‘yan wasansu kudaden da ya kamata a basu kafin fara gasar lashe kofin duniya ta mata a gobe. AFP
Talla

Kowace ‘yar wasa da za ta fafata a gasar za ta samu dala dubu 30, wanda a baya hukumar ta ce z ata tura musu kudinsu kai tsaye, ba sai ya bi ta hannun hukumomin kasashensu ba, sai dai hakan ba ta samu ba.

Hukumar FIFA ta ware dala miliyan dari da 10 don rabawa ‘yan wasan kasashen 32 da suka samu gurbi a gasar ta bana, kari akan dala miliyan 30 da ta ware wa gasar ta shekarar 2019 da kuma dala miliyan 15 a gasar ta shekarar 2015.

A gasar lashe kofin duniya ta maza da aka yi a shekarar da ta gabata a Qatar, hukumar FIFA ta rabawa ‘yan wasan kasashe 32 kyautar dala miliyan 440.

Infantino ya sha alwashin ganin hukumar ta dai-daita yawan kudaden da ‘yan wasa maza da mata ke samu a gasar lashe kofin duniya na bangarorin da ke tafe a shekarun 2026 da kuma 2027.

A gobe ne dai kasashen Australia da New Zealand za su bude gasar, inda Australia ta kara da Norway ita kuma New Zealand ta kara da Ireland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.