Isa ga babban shafi

Infantino ya sake lashe zaben shugabancin hukumar FIFA

A Alhamis din nan ne aka sake zaben Gianni Infantino a matsayin shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duyina FIFA, inda zai ci gaba da jagorantar ta har nan da shekarar 2027.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Gianni Infantino.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Gianni Infantino. REUTERS - JEAN BIZIMANA
Talla

A karo na uku ke nan Infantino mai shekaru 52 a duniya da ya gaji Sepp Blatter a shekarar 2016, ke samun nasarar lashe zaben shugabancin hukumar, bayan amincewa da shi da wakilan da ke zaben shugaban hukumar 211 suka yi.

Duk da cewa dokokin hukumar sun fayyace wa’adi 3 na shekaru hur-hudu na shugabantar hukumar, amma Infantino na shirin ci gaba da jagorantar FIFA har zuwa shekarar 2031, domin a cewarsa shekaru ukun farko da ya yi bai cikin lissafi.

A karkashin jagorancinsa, hukumar ta FIFA ta kara yawan kungiyoyin da ke halartar gasar lashe kofin duniya ta maza daga 32 zuwa 48 wanda za a fara amfani da tsarin a gasar ta shekarar 2026, haka nan a karon farko gasar lashe kofin duniya ta mata ita ma aka kara yawan kasashen da ke halartar ta zuwa kungiyoyi 32, kuma a gasar da za a yi a wannan shekarar da kasashen Australia da New Zealand za su karbi bakunci za a fara amfani da tsarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.