Isa ga babban shafi

FIBA na bincike kan yadda 'yan wasan kwallon kwandon Mali suka dambace

Hukumar kula da kwallon kwando ta duniya FIBA,  ​​ta fara bincike kan dalilin da ya sanya wasu ‘yan wasan kasar Mali bai wa hammata iska, jim kadan bayan kammala wasa a gasar cin kofin kwallon Kwando ta duniya.

'Yan wasan kwallon kwando na kasar Mali yayin wasan da ta kai ga dambacewa.
'Yan wasan kwallon kwando na kasar Mali yayin wasan da ta kai ga dambacewa. Getty Images - Jason McCawley
Talla

Rikicin ya barke ne jiya litinin a yayin da manema labarai ke yin hira da Sassa Cado ‘yar wasan kwallon Kwando ta kasar Serbia, bayan lallasa kasar Malin da suka yi da ci 81-68, a birnin Sydney.

Wani gajeren faifan bidiyo da aka yada, ya nuna Salimatou Kourouma ta kasar Mali yayin da take dirkawa abokiyar wasanta naushi sau uku a jere, kafin daga bisani sauran ‘yan wasa su shiga tsakani.

Hukumar FIBA ta ce da zarar ta kammala bincike za ta yanke shawara kan matakan ladabtarwar da ya dace ta dauka.

Har yanzu dai Mali ba ta yi nasara a gasar cin kofin duniya ta kwallon Kwando ba, kuma za ta kara ne da Canada a wasan karshe na matakin rukuni a yau Talata.

Karo na biyu kenan da Mali ta samu halartar gasar kwallon Kwando ta duniya, bayan samun damar maye gurbin Najeriya, wadda ta fice saboda matsalolin gudanar da harkokin wasan kwallon kwandon a cikin gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.