Isa ga babban shafi

Najeriya tayi amai ta tande kan daina shiga wasannin kwallon kwando

Najeriya tayi amai ta tande wajen soke janyewar da tayi na shiga wasannin kwallon Kwando na shekaru 2 sakamakon rikicin shugabancin da ya dabaibaye hukumar gudanarwar kungiyar ta kasa.

'Yan wasan kwallon kwandon Najeriya na tawagar D'Tigress.
'Yan wasan kwallon kwandon Najeriya na tawagar D'Tigress. © AFP
Talla

Bayan sukar da ya biyo bayan janyewar Najeriyar daga wasannin na shekaru 2 daga ciki da wajen kasar, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bukatar soke dakatarwar da kuma ci gaba da shiga wasannin a matakai daban daban na duniya.

Jami’in ma’aikatar wasanni na kasar Ismaila Abubakar ya sanar da sauyin da aka samu bayan amincewar shugaban kasa, abinda ke nuna cewar yanzu haka Najeriya zata ci gaba da shiga wasanni kwallon Kwando a matakin Afirka ta Yamma da nahiyar Afirka da kuma duniya baki daya.

A watan Janairun da ya gabata Najeriya ta fada rikicin shugabancin kungiyar kwallon kwandon na kasa, lokacin da bangarori guda biyu suka gudanar da tarurruka daban daban wanda suka kaiga samun shugabanni guda biyu, wato Musa Kida da Igoche Mark.

Tuni matakin ya sanya Najeriya rasa gurbin shiga gasar mata ta duniya da za’ayi a kasar Australia, yayin da hukumar ta duniya tayi barazanar daukar matakin ladabtarwa akan kasar.

Buhari ya bukaci masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kwandon da su gaggauta warware rikicin shugabancin da ya sanya daukar wancan mataki na janyewa daga wasannin da gwamnati ta yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.