Isa ga babban shafi

Ecuador na fuskantar hadarin rasa damar taka leda a gasar cin kofin Duniya

Tawagar kwallon kafar Ecuador na cikin hatsarin fuskantar hukuncin fitar da ita daga gasar cin kofin duniya, biyo bayan binciken kafar labaran wasanni ta Sportsmail da ya gano sabuwar hujjar dake tabatar da cewar wani dan wasan kasar ta Ecuador ya yi amfani da takardar shaidar haihuwa ta bogi, a wani bincike da hukumar kwallon kafa ta kasarsa ta yi kokarin rufewa.

Cikin watan Nuwamba mai zuwa ne ake saran fara gasar ta cin kofin duniya.
Cikin watan Nuwamba mai zuwa ne ake saran fara gasar ta cin kofin duniya. © Shutterstock
Talla

Sakamakon binciken bazatan da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta gudanar akan batun dan wasa Byron Castillo na zuwa ne kwanaki kadan kafin kotun daukaka karar wasanni ta duniya ke shirin yanke hukunci a kai a ranar Alhamis dake tafe.

Hukuncin dai zai iya canza kasar da Qatar za ta buga a wasan farko na gasar cin kofin duniya da ita.

Castillo, dan wasan dake bugawa tawagar Ecuador bangaren tsaron baya,  ya buga wasanni takwas na neman tikitin halartar gasar cin kofin duniya.

Cikin wani sauti da kafar Sportsmail ta fitar a yau na hirar da Castillo ya yi da masu bincike shekaru hudu da suka wuce, ya ce a shekarar 1995 aka haife shi, a maimakon shekarar 1998 dake rubuce a takardar shaidar haihuwarsa ta Ecuador.

A bangaren suna kuwa, dan wasan ya ce, cikakken sunansa shi ne Bayron Javier Castillo Segura, a maimakon Byron David Castillo Segura wanda ya bayyana akan takardar shaidar haihuwarsa.

Wani batu da hukumar FIFA ke bincike akai kuma shi ne tantance ainahin kasa ko mahaifar dan wasan wanda wasu majiyoyi suka ce a kasar Colombia aka haife shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.