Isa ga babban shafi
FIFA-Gasar cin kofin Duniya

Jadawalin kasashe 32 da suka samu tikitin zuwa gasar cin kofin Duniya a Qatar

Hukumar FIFA ta fitar da jadawalin wasannin gasar cin kofin Duniya na karawar kasashe 32 ko da ya ke 29 daga cikinsu ne kadai suka san makomarsu, yayinda sauran ke dakon wasannin watan Yuni gabanin sanin inda suka dosa.

Jadawalin gasar cin kofin Duniya.
Jadawalin gasar cin kofin Duniya. © Studio graphique FMM
Talla

Rukunin A na jadawalin na kunshe da kasashen Qatar mai masaukin baki kana Ecuador da Senegal zakarar Afrika da kuma Netherlands.

Rukunin B na kunshe da kasashen Ingila da Iran da Amurka da kuma kasashen ko dai Wales ko Scotland ko kuma Ukraine, sai dai wadda ta yi nasara a karawar watan na Yuni tsakanin kasashen 3, saboda yadda aka dakatar da wasansu sakamakon rikicin Ukraine.

A rukunin C, akwai kasashen Argentina da Saudi Arabia da Mexico da kuma Poland.

Rukunin D na kunshe da kasashen Faransa mai rike da kambu da Denmark sai Tunisia, sai kuma daya daga cikin kasashen ko dai hadaddiyar daular larabawa ko Australia ko kuma Peru.

Rukunin E na kunshe da Spain da Jamus da Japan kana kasashen ko dai Costa Rica ko New Zealand

A rukunin F akwai kasashen Belgium da Canada da Morocco da kuma Croatia.

Sai rukunin G da ya kunshi Brazil da Serbia da Switzerland da kuma Kamaru

Kana rukunin karshe na H da ke dauke da kasashen Portugal da Ghana da Uruguay da kuma Korea ta kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.