Isa ga babban shafi

Zan yanke shawara kan lamurra da dama bayan gasar cin kofin duniya - Messi

Lionel Messi ya bayyana cewa ba shi da tabbas game da makomarsa, inda zai yanke shawara kan al’amura da dama bayan kammala gasar cin kofin duniya da kasar Qatar za ta karbi bakunci.

Lionel Messi
Lionel Messi Pool via REUTERS - MIGUEL GUTIERREZ
Talla

Messi ya bayyana haka ne a lokacin ganawa da manema labarai, jim kadan bayan wasan neman tikitin halartar gasar cin kofin duniya da suka lallasa Venezuela da kwallaye 3-0, wanda dan wasan ya ci daya daga ciki.

Kwallon da Messi ya ci, ita ce ta 81 a wasanni 158 da ya bugawa tawagar kasar.

Lionel Messi
Lionel Messi © REUTERS/Benoit Tessier

Wannan kakar dai ta kasance mai wahala ga Messi bayan da ya gaza haskawa wajen nuna bajinta kamar yadda aka saba gani tun bayan da ya koma kungiyar Paris Saint-Germain daga Barcelona.

A shekarar bara ne dai tauraron dan kwallon na Argentina ya jagoranci kasarsa zuwa nasarar lashe kofin gasar Copa America.

Sai dai, yayin da tsohon dan wasan Barcelona ke ci gaba da samun nasara tare da tawagar kasarsa Argentina, har yanzu bai samu yadda yake so a Faransa ba, inda ya zira kwallaye biyu kacal a gasar Ligue 1, kwallaye biyar kuma a gasar zakarun Turai, yayin da ya gaza taimakawa PSG wajen hana fitar da ita a zagaye na biyu, a gasar cin kofin Zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.