Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Kocin Brazil zai ajje aiki bayan gasar cin kofin Duniya ta Qatar

Mai horar da tawagar kwallon kafar Brazil Adenor Leaonardo Bacchi da aka fi sani da Tite ya sanar da shirin yin murabus bayan kammala gasar cin kofin Duniya da za ta gudana a Qatar.

Tawagar kwallon kafar Brazil.
Tawagar kwallon kafar Brazil. Pool via REUTERS - RODRIGO BUENDIA
Talla

A wata zantawarsa ta SportTV Titte mai shekaru 60 ya ce zai jagoranci Brazil zuwa Qatar amma da zarar sun dawo aikinsa y agama.

Brazil wadda ta dage kofin Duniya har sau 5 a tarihi a wannan karonma na cikin tawagogin da ake yiwa hasashen yiwuwar su kai labari la’kari da irin rawar da ‘yan wasanta ke takawa a lig lig din Turai.

Cikin kalaman kocin wanda y afara horar da Brazil tun daga shekarar 2016 yana fatan kafa tarihin kawowa kasar kofin duniya na 6.

Brazil dai ta dage kofin duniya ne a shekarun 1958 da 1962 da kuma 1994 kana shekarar 2002, kuma tun daga wancan lokaci ne ta fara fuskantar koma baya a fagen tamaula gabanin zuwansa a 2016 da ya dawo da martabar kasar har ta iya kaiwa wasan gab da na karshe a Rasha yayin gasar cin kofin duniya na 2018 gabanin rashin nasara hannun Belgium da kwallo 2 da 1 wanda ek da nasaba da raunin tauraron kasar wato Neymar Junior.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.