Isa ga babban shafi
Wasanni-Gasar kofin Duniya

Brazil ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin Duniya ta 2022

Brazil ta samu gurbi a gasar cin kofin Duniya ta 2022 da za ta gudana a Qatar inda ta zama kasa ta 4 da zuwa yanzu ta samu wannan gurbi kuma ta farko daga kudancin Amurka.

Lucas Paqueta mafi zura kwallo a Brazil tare da Vinicius Junior da kuma Neymar yayin murnar zura kwallo a ragar Colombia da ya baiwa kasar damar samun tikiti a gasar cin kfoin duniya.
Lucas Paqueta mafi zura kwallo a Brazil tare da Vinicius Junior da kuma Neymar yayin murnar zura kwallo a ragar Colombia da ya baiwa kasar damar samun tikiti a gasar cin kfoin duniya. NELSON ALMEIDA AFP
Talla

Kasashen da zuwa yanzu ke da tikitin gasar sun kunshi Qatar mai masaukin baki da Jamus mai tarihin dage kofin sau 4, kana Denmark tukuna ita Brazil din bayan wasanta na yau da ta yi nasara kan Colombia da kwallo 1 mai ban haushi.

Brazil na matsayin mafi tarihin dage kofunan gasar ta cin kofin Duniya bayan dage shi har sau 5 tsakanin shekarun 1958 da 1962 da kuma 1970 baya ga shekarar 1994 da 2002.

Haka zalika kasar ta Brazil na jerin kasashen da basu taba fashin samun tikiti a gasar ta cin kofin Duniya ba tun bayan farota a shekarar 1930.

Gasar ta cin kofin Duniya bisa al’ada na kunsar tawagar kasashe 32 tun bayan fadadata a shekarar 1998, a wannan karon za ta faro ne daga ranar litinin 21 ga watan Nuwamban 2022 zuwa ranar lahadi 18 ga waran Disamban shekarar inda kasashe 31 kan fafatawa don gurbin yayinda mai masauki baki ke samun gurbi a bagas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.