Isa ga babban shafi
Brazil-Argentina

Argentina da Brazil za su hadu da fushin hukumar FIFA

Hukumar FIFA ta ce kwamitinta na ladabtarwa yanzu haka ya fara shirye-shiryen hukunta kasashen Argentina da Brazil bayan takaddamar da ta kai ga dakatar da wasansu na neman gurbin shiga gasar cin kofin Duniya a makon jiya.

Tawagar 'yan wasan Brazil da na Argentina bayan dakatar da wasansu na ranar lahadi.
Tawagar 'yan wasan Brazil da na Argentina bayan dakatar da wasansu na ranar lahadi. NELSON ALMEIDA AFP
Talla

Mintuna kalilan bayan fara wasan kasashen biyu na ranar lahadi ne aka dakatar da shi, bayan da ma’aikatar lafiyar Brazil ta yi zargin wasu ‘yan wasan Argentina 3 sun karya dokokin covid-19 ta hanyar kin killace kansu bayan isowarsu.

A cewar Fifa hukuncin zai kasance bisa ga bayanan da jami'anta suka tattara a lokacin faruwar lamarin a filin wasa na Sao Paulo da ke brazil.

Bayan matakin dakatar da wasan dai babu bayani kan ranar da za a gudanar da shi har zuwa yanzu.

Bisa ga dokokin Brazil din, duk matafiyin da ya shiga kasar daga birtaniya dole ya killace kansa na kwanaki 14, wanda kuma bayanani ke cewa wasu 'yan wasan Argentina da ba a bayyana sunansu ba sun ki mutunta tsarin.

Yanzu haka Brazil na jiran haduwarta da Bolivia ne ranar juma’ar nan 10 ga watan Satumba duk dai a wasannin na neman gurbin shiga gasar cin kofin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.