Isa ga babban shafi
Wasanni

An soke wasan Argentina da Brazil saboda dokokin korona

An soke wasan cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta Brazil da Argentina jim kadan bayan fara wasan, sakamakon takaddama kan ka'idojin korona.

Gwarazan 'yan wasan kwallon kafar Duniya Messi na Argentina da Neymar na Brazil.
Gwarazan 'yan wasan kwallon kafar Duniya Messi na Argentina da Neymar na Brazil. MAURO PIMENTEL AFP/Archivos
Talla

‘Yan wasan Argentina sun fice daga filin wasan, bayan da jami'an lafiya na Brazil suka shiga filin suka dakatar da karawar ta hamayya, sai kuma aka ga kyaftin din Agentina Lionel ya sake fitowa amma ba tare da rigar tawagar ba.

Cece-kucen mai ban mamaki ya biyo bayan da jami'an lafiya suka ce ya zama tilas wasu 'yan wasan Argentina hudu da ke taka leda a Ingila su killace kan su har na tsawon kwanaki 14 kamr yadda dokokin korona na kasar suka tanadar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.