Isa ga babban shafi
Kwallon kafa-Maradona

Likitocin Argentina 7 na fuskantar tuhuma kan sakaci da lafiyar Maradona

Gwamnatin Kasar Argentina ta kaddamar da bincike a kan likitoci guda 7 da suka duba tsohon tauraron kwallon kafar kasar Diego Maradona wadanda ake zargi da sakaci wajen mutuwar sa a shekara da ta gabata.

Tauraron kwallon Argentina Diego Maradona.
Tauraron kwallon Argentina Diego Maradona. ALEJANDRO PAGNI AFP/Archives
Talla

Likitocin da ke fuskantar tuhumar kisan kai bada niyya ba sun hada da Leopoldo Luque da Agustina Cosachov da Carlos Diaz kuma suna fuskantar hukuncin daurin tsakanin shekaru 8 zuwa 25 a gidan yari idan an tabbatar da laifi akan su.

Wannan sabon binciken ya biyo bayan sakamakon rahotan wasu kwararru suka gudanar kan abinda ya yi sanadiyar mutuwar tauraron kwallon kafar wanda ya gamu da bugun zuciya bayan ya cika shekaru 60 a duniya.

Rahotan binciken ya bayyana cewar Maradona bai samu kulawar da ta dace ba lokacin da ya gamu da bugun zuciyar, yayin da jami’an kula da lafiyar su ka bar shi cikin mawuyacin hali.

Hukumomin kasar sun haramtawa jami’an kiwon lafiyar 7 barin kasar, yayin da alkalai za su musu tambayoyi daga ranar 31 ga wannan wata zuwa 14 ga watan Yuni.

Binciken ya biyo bayan korafin da wasu daga cikin ‘yayan Maradona suka gabatar akan likitan mahaifin nasu wadanda suka zarga da kin kula da shi gabanin mutuwar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.