Isa ga babban shafi
Argentina-Maradona

An yi sakaci da jinyar Maradona gabanin mutuwarsa - kwararru

Kwamitin da aka kafa domin gudanar da bincike a kan abin da yayi sanadiyar mutuwar tauraron kwallon duniya kuma dan kasar Argentina, Diego Maradona ya ce tsohon kaftin din kasar bai samu kulawar da ta dace ba, ganin yadda aka bar shi yana fama da ciwo kafin rasuwar sa.

Tsohon gwarzon dan wasan duniya dan kasar Agentina marigayi  Diego Maradona
Tsohon gwarzon dan wasan duniya dan kasar Agentina marigayi Diego Maradona Marcos Brindicci/AP Photo
Talla

Rahotan kwamitin binciken mai shafuka 70 ya ce Maradona wanda ya rasu sakamakon bugun zuciya  a ranar 25 ga watan Nuwambar bara yana da shekaru 60, ya kama hanyar mutuwa sa’oi 12 kafin mutuwar sa.

Masana guda 20 da suka gudanar da bincike a karkashin umurnin mai gabatar da kara domin gano abin da ya kashe shi saboda zargin sakacin likita sun ce tsohon tauraron duniyar bai samu kulawar da yake bukata ba.

Yanzu haka likitansa Leopoldo Luque da mai kula da masu tabin hankali Agustina Cosachov da Carloz Diaz mai kula da halayr ‘dan Adam na fuskantar tuhuma tare da wasu masu taimaka wa likita guda biyu da shugabar su da kuma jami’in kula da lafiya na asibitin da aka kai shi.

Rahotanni sun ce sakamakon binciken na iya haifar da zargin aikata kisa bada niyya ba wanda ke dauke da hukuncin daurin shekaru 15 idan kotu ta tabbatar.

Wannan bincike ya biyo bayan korafin da biyu daga cikin yayan matan Maradona guda 5 suka shigar a kan likita Luque wanda suke zargi da tabarbarewar lafiyar mahaifinsu bayan aikin da aka masa a kwakwalwa.

An dai yi wa Maradona aikin ne a ranar 3 ga watan Nuwamnar bara, kwana 4 bayan ya yi bikin cika shekaru 60 da haihuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.