Isa ga babban shafi
Wasanni-Argentina

Kotu ta bada umarnin adana gawar Maradona saboda kwayoyin halittarsa

Wata kotu a Argentina ta bada umarnin bada kariya ta musamman ga gawar tauraron kwallon kafa na duniya Diego Maradona ta hanyar adana ta.

Marigayi Diego Maradona na kasar Argentiana
Marigayi Diego Maradona na kasar Argentiana REUTERS/Henry Romero
Talla

A cewar kotun ta bada umarnin adana gawar ta Maradona ce, saboda daukar kwayar halittarsa idan bukatar hakan ta taso ta fuskar neman tabbatar da ikirarin da wasu ka iya yi na zama ‘ya’yan gwarzon na duniyar tamaula.

Sai dai lauyoyin tsohon dan wasan kungiyoyin Napoli da Boca Juniors sun ce babu bukatar hukuncin kotun na adana gawar maigidan nasu marigayi, domin kuwa tuni aka dauki kwayoyin halittarsa aka kuma adana domin irin wannan rana.

A ranar 25 ga watan Nuwamba Maradona ya mutu bayan fama da bugun zuciya, aka kuma binne shi a wata makarbarta dake wajen babban birnin kasar Argentina Buenos Aires.

Kawo yanzu baya ga ‘ya’yan Maradona 5 da aka sani, wata matashiya yar shekaru 25 mai suna Mahali Gil ta yi ikirarin zama ‘ya ga marigayin, wanda tace bata gano cewar ‘yar sa ba ce sai a shekaru 2 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.