Isa ga babban shafi
Wasanni

An fara zaman makoki a Argentina kan mutuwar Maradona

An fara zaman makoki na tsawon kwanaki uku a Argentina domin jimamin mutuwar tsohon tauraron dan kwallon duniya Diego Marado wanda ya yi ban-kwana da duniya a ranar Laraba yana da shekaru 60 sakamakon bugun zuciya.

Masoya Maradona na alhinin mutuwarsa a Argentina
Masoya Maradona na alhinin mutuwarsa a Argentina Reuters
Talla

Tuni aka shinfide gawarsa a katafaren ginin Casa Rosada da ke fadar shugaban kasar Argentina domin bai wa jama’a damar karrawa ta karshe ga dan wasan.

Yanzu haka daruruwan mutane sun fara jeruwa akan layi don ganin gawar tasa daya bayan daya.

Tuni aka dage wasa tsakanin Sport Club International da kuma tsohuwar kungiyar Maradona wato Boca Juniors domin karrawa ga marigayin.

Masoyansa sun yi dafifi a filin wasa na Boca Juniors da ke birnin Buenos Aires, inda akasarinsu ke ta rusa kuka shame-shame saboda bakin cikin mutuwarsa.

Haka ma a Italiya, masoyan Maradona sun cika makil a harabar filin wasa na Napoli, yayin da aka kunna wuta don karramawa ga marigayin wanda ya zura kwallaye 81 a wasanni 188 da ya buga wa kungiyar kwallon kafa ta Napoli.

Maradona ya taka leda a kungiyoyin kwallon kafa irinsu Barcelona da Napoli, sannan shi ne kyaften din tawagar Argentina wadda ta lashe kofin duniya a 1986, inda a wancan lokacin aka zarge shi da yin amfani da hannu wajen jefa kwallo a ragar Ingila a matakin kwata fainal na gasar.

Maradona ya mutu ne makwanni da yi masa tiyata a cikin kokon kansa sakamakon daskarewar jini a kwakwaluwarsa, sannan ya yi fama da masifar kwankwadon barasa da hodar ibilis.

Kodayake mai shigar da kara na gwamnatin Argentina ya ce, za a gudanar da gwajin kan gawarsa.

Tuni tsoffin ‘yan wasa har ma da wanda ke kan ganiyarsu suka fara aikewa da sakon ta’aziyar rashin Maradona, inda Pele da ake kallo a matsayin babban abokin hamayyarsa ya ce, yana fatan za su hadu wata rana a lahira don murza tamola.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.