Isa ga babban shafi
Brazil-wasanni

FIFA ka iya hukunta 'yan wasan Brazil 9 saboda kungiyoyinsu na Turai

Da yiwuwar hukumar FIFA ta iya dakatar da ‘yan wasan Brazil da kungiyoyinsu suka gaza basu damar dokawa kasarsu wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Duniya a karshen makon nan.

Tawagar 'yan wasan Brazil.
Tawagar 'yan wasan Brazil. MARTIN BERNETTI AFP
Talla

Kungiyoyin Firimiya 6 da ke dauke da manyan ‘yan wasan Brazil yanzu haka na neman karin haske don yanke hukunci nan da sa’o’I 24 da nufin kaucewa hukuncin na FIFA da zai iya kaiwa ga dakatarwar kwanaki 5 a karshen kaka.

Zuwa yanzu ‘yan wasan Firimiya 9 Brazil ta sanya a jerin wadanda za su taka mata leda a wasannin neman gurbin, ciki kuwa har da mai tsaron ragar Liverpool Alisson Becker da Fabinho da kuma Firmino, sai ‘yan wasan Manchester City Ederson da kuma Gabriel Jesus kana Thiago Silver na Chelsea da Fred na Manchester United sai Raphinha na Leeds da dan wasan gaba na Everton Richarlison.

Shugaban hadakar kungiyoyin kwallon kafar Turai, Charlie Marshall ya ce kungiyoyin na da sa’o’I 24 don sanin ko za su iya wasannin wannan mako da ‘yan wasansu na Brazil ko akasin haka.

Har zuwa yanzu dai FIFA ba ta sanarwar kungiyoyin yiwuwar dakatar da ‘yan wasan ba idan suka gaza halartar wasan.

Karkashin dokokin yaki da covid-19 dai, matukar ‘yan wasan suka halarci wasannin a Brazil kenan suna bukatar kwanaki 10 idan sun dawo don su killace kansu gabanin fara wasa, wanda ke nuna kungiyoyin za su yi asarar kwanaki fiye da mako biyu ga ‘yan wasan dai dai lokacin da wasannin firimiya suka kankama.

A cewar Marshall a yanayin da ake ciki akwai bukatar FIFA ta tausayawa kungiyoyi wajen basu damar iya hana ‘yan wasan dokawa kasashen wasannin saboda yadda za su rasa damar dokawa kungiyoyinsu wasanni masu muhimmanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.