Isa ga babban shafi

Qatar ta ce ba za ta lamunci badala yayin gasar cin kofin duniya ba

Qatar ta haramtawa baki ‘yan kallo yin casu ko kuma kebewa da ba muharraman su ba, lokacin gasar cin kofin duniya ta 2022 yayin da kasar mai masaukin baki ta ce za ta tilasta dakatar da shan giya da jima'i tsakanin wadanda ba ma’aurata ba.

© AP - Hassan Ammar
Talla

Kasar Qatar dai ta dade da haramta yin jima'i tsakanin marasa aure da kuma shan barasa a bainar jama'a, wanda ya yi daidai da akidar Shari'a, kuma wadanda suka karya dokar za su fuskanci zaman gidan yari na tsawon shekaru bakwai.

A cewar jaridar Daily Star, kasar na shirin aiwatar da dokar haramta shan barasa, kebewa tsakanin wadanda ba ma’aurata ba ga baki ‘yan kasashen waje da za su kasance a kasar domin halartar kallon gasar cin kofin duniya.

Kasar dai ta tsaurara matakai inda yanzu haka baya ga rashin cudanya tsakanin mata da maza, ma’aurata ma ba za su nuna soyayya a zahiri ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.