An nemi sayen tikitin gasar cin kofin duniya ta bana kusan miliyan 24 - FIFA
Hukumar FIFA ta ce an nemi tikitin shiga filaye don kallon wasannin gasar cin kofin duniya miliyan 23 da dubu 500, yayin da ya rage kasa da watanni 7 babbar gasar ta fara gudana a kasar Qatar.
Wallafawa ranar:
Rahoton na FIFA, ya ce bukatar tikitan kallon wasannin na gasar cin kofin duniya ya fi yawa daga kasashen Argentina, da Brazil, da Ingila, da Faransa, da Mexico. Sai kuma mai masaukin baki, wato kasar ta Qatar, da Saudiya da kuma Amurka.
Hukumar ta FIFA ta kara da cewar, farashin tikitin gasar cin kofin duniyar ta bana, ya karu da kusan kashi 30 cikin 100 idan aka kwatanta da na gasar da Rasha ta karbi bakunci a shekarar 2018.
Tikiti mafi arha a bana dai na 'yan Qatar ne da kuma bakin-hauren da ake aiki a kasar, wadanda za su biya dala 10 kacal don kallon wasannin zagayen farko na matakin rukuni.
Sai dai fa a wasan karshe, farashin tikiti mafi tsada ya zarce da dala dubu 1,600, kwatankwacin naira 664,304 a kudin Najeriya, abinda ke nufin an samu karin kashi 45 cikin 100 kan farashin da aka gani a shekarar 2018.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu