Isa ga babban shafi
Qatar

Babu nisa tsakanin filayen wasannin da za a yi Qatar 2022

A kasar Qatar za a gudanar da wasannin gasar cin kofin duniya a shekarar 2022 a filayen wasannin da ba su da wata tazara mai nisa a tsakaninsu.

A watan Nuwamba zuwa Disemba na 2022 ne za a gudanar da Qatar 2022
A watan Nuwamba zuwa Disemba na 2022 ne za a gudanar da Qatar 2022
Talla

Filaye mafi nisa da za a yi wasannin ba su wuce nisan kilomita 55 ba wato kwatankacin nisan da ya raba filayen Old Trafford na Manchester United da kuma Anfield filin wasan Liverpool.

Sannan filaye mafi kusanci su ne na al Bayt da al Khor da ba su wuce nisan kilomita 5 ba a tsakaninsu, wato kamar tazarar da ke tsakanin filin Emirate na Arsenal da White Hart Lane na Tottenham da ke makwabtaka da juna a London.

Wannan dai ya yi sabani da Brazil inda tazara mafi kusanci tsakanin filayen wasannin shi ne nisan kilomita kusan 400. Yayin da tazara mafi nisa shi ne nisan kilomita sama da 3000.

Kwamitin shirya wasannin a Qatar ya ce wannan dama ce ga masoya kwallon kafa su kalli wasanni fiye da daya a rana.

A Qatar dai za a gudanar da gasar cin kofin duniyar ne a tsakanin watan Nuwamba zuwa Disemba sabanin watannin Yuni zuwa Yuli da aka saba gudanar da gasar.

An sauya lokacin gasar ne a Qatar saboda zafi da ake dadawa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.