Isa ga babban shafi

Afrika ta kudu ta shiga gaban Najeriya a yawan lambobin yabo a gasar Commonwealth

Ana ci gaba da fafata wasannin motsa jiki na Commonwealth da ke gudana a birnin Birmingham a Ingila, inda tuni tawagogin ‘yan wasa suka tarawa kasashen da su ke wakilta jerin lambobin yabo na Zinare, Azurfa da kuma Tagulla.

Yadda wasannin kwallon kafa karkashin gasar Commonwealth ke gudana.
Yadda wasannin kwallon kafa karkashin gasar Commonwealth ke gudana. POOL/AFP
Talla

Kasar Australia ke kan gaba da jumullar lambobin yabo 123 da suka hada da Zinare 46, Azurfa 38 da kuma Tagulla 39, sai mai masaukin baki Ingila da ke da Zinare 39, Azurfa 37 da kuma Tagulla 29, jumillar lambobin yabo 105.

Canada ce kasa ta Uku da lambobi 57, Zinare 16, Azurfa 20 da Tagullla 21.

Daga nahiyar Afirka, Afirka ta Kudu ce ta farko a nahiyar, amma ta 6 a gasar ta Commonwealth bayan samun lambobin yabo 20, da suka kunshi Zinare 6, Azurfa 7 da Tagullla 7.

Sai kuma Najeriya ta biyu a Afirka, amma ta goma a gasar motsa jikin ta kasa da kasa, bayan samun jumillar lambobin yabo 8, da suka hada da Zinare 3, Azurfa 1 da kuma Tagullla 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.