Isa ga babban shafi

'Yar tseren Najeriya Tobi Amusan ta zaman zakarar Duniya a gudun mita 100

‘Yar tseren Najeriya Tobi Amusan ta zama zakarar duniya bayan lashe zinare a tseren mita 100 na tsallen shinge a gasar da aka kammala jiya lahadi a birnin Oregon na kasar Amurka.

'Yar tseren Najeriya Tobi Amusan.
'Yar tseren Najeriya Tobi Amusan. REUTERS - MIKE SEGAR
Talla

Amusan da ta kafa tarihin kasancewa wadda ta tsallake matakin wasan gab da na karshe a dakika 12 da digo 12 a zagayen farko kana dakika 12 da digo 6 a zagaye na 2 yayin wasanta a filin Hayward ta sha gaban ‘yar Jamaica Britany Anderson da ta zo ta biyu bayan kare nata gudun a dakika 12 da digo 23 kana Jasmine Camacho-Quinn ta Puerto Ribo a matsayin ta 3.

Sai dai mahukuntan gasar sun ce baza a sanya nasarar ta Amusan a jerin wadanda suka kafa tarihin Duniya ba, la’akari da yadda aka samu nasarar gudun mita 2 da rabi a dakika guda.

Amusan ‘yar Najeriya ta yi nasarar karbe kambun ne daga hannun Keni Harrison ‘yar Amurka da ke rike da shi tun shekarar 2016.

A jawabinta bayan nasara a tseren, Amusan ta ce ko shakka babu ta yarda da kanta amma ba ta yi tsammanin zama zakarar Duniya nan kusa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.