Isa ga babban shafi
Wasanni

PSG ta lallasa Marseille: Mbappe ya samu rauni

Kungiyar PSG ta lallasa Marseille da kwallaye 3-0 karo na biyu cikin kwanaki hudu, nasarar da ta bata damar kai wa ga zagayen kusa da na karshe a gasar cin kofin Faransa.

Dan wasan gaba na kungiyar PSG, Kylian Mbappe.
Dan wasan gaba na kungiyar PSG, Kylian Mbappe. REUTERS/Charles Platiau
Talla

Dan wasan gaba na kungiyar Angel Di Maria ne ya ci kwallaye 2, sai Edinson Cavani ya jefa ta uku a minti na 81.

Sai dai fa an yi ba ai ba, wai an jefa agwagwa a ruwa, domin kuwa matashin dan wasan kungiyar ta PSG na gaba Kylian Mbappe ya fice daga fili kafin kammala wasan sakamakon raunin da ya samu, abinda ya sa fargaba kan raguwar karfin kungiyar a karawar da zata yi da Madrid mako mai zuwa a gasar zakarun nahiyar turai.

A ranar Lahadin da ta gabata dan wasan PSG mafi tsada a duniya Neymar ya samu rauni a kafarsa, a wasan Ligue 1, da suka lallasa Marseille da 3-0, rauni da ya tabbata cewa Neymar ba zai buga was aba tsawon makwanni 6.

Sai dai har yanzu ana dakon bayyana sakamakon binciken likitoci don tantance girman raunin da Mbappe ya samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.