Isa ga babban shafi
Wasanni

"Neymar yana bukatar tiyata cikin gaggawa"

Mahaifin dan wasan gaba na PSG Neymar, ya bukaci kungiyar ta gaggauta amincewa da yi wa dan nasa tiyata a kafa sakamakon raunin da ya samu.

Neymar, a lokacin da ya samu rauni a wasan da ya gudana tsakanin kungiyar Paris St Germain da Olympique de Marseille.
Neymar, a lokacin da ya samu rauni a wasan da ya gudana tsakanin kungiyar Paris St Germain da Olympique de Marseille. REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Neymar ya samu raunin ne a wasan da suka lallasa kungiyar Marseille da kwallaye 3-0 a ranar Lahadi, kuma da farko an yi zaton gurdewa ya yi a kafa.

Daga bisani ne likitoci suka gano cewa ya samu tsagewar kashin kafarsa da ke hade da ‘yan yatsu Metatarsals a turance.

Mahaifin Neymar ya tabbatar da cewa dan nasa zai jiyyar akalla makwanni 6, wanda hakan ke nuna babu damar ya buga wasan zakarun nahiyar turai tsakanin PSG da Madrid.

Sai dai a gefe guda mai horar da PSG Unai Emery, ya musanta cewa Neymar yana bukatar a yi masa tiyata, kuma akwai yi wuwar dan wasan ya samu damar faffatawa a wasan da zasu yi da Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.