Isa ga babban shafi
wasanni

Neymar ka iya warkewa kafin wasan PSG da Real madrid

Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta ce har yanzu bata fidda tsammanin dan wasan gabanta Neymar Junior zai samu damar halartar wasan da za su fafata da Real Madrid a gasar zakaru ta kungiyoyi 16 da suka yi saura.

Neymar dai ya samu rauni ne a wasan da suka yi nasara kan Marseille da ci  3- ba ko daya a gasar Lig 1 ta Faransa a ranar Lahadi.
Neymar dai ya samu rauni ne a wasan da suka yi nasara kan Marseille da ci 3- ba ko daya a gasar Lig 1 ta Faransa a ranar Lahadi. REUTERS/Stephane Mahe
Talla

A cewar Kocin PSG Unai Emery, dan wasan mafi tsada a duniya dan brazil mai shekaru 26 ka iya warwarewa gabanin wasan da za su fafata da Real Madrid a ranar 6 ga watan Maris mai kamawa.

Neymar dai ya samu rauni ne a wasan da suka yi nasara kan Marseille da ci 3- ba ko daya a gasar Lig 1 ta Faransa a ranar Lahadi, a dai dai lokacin da ya rage saura kwanaki 9 su kara da Real Madrid gasar cin kofin zakarun Turai zagaye na biyu.

Tuni dai Kochin RealMadrid Zinadine Zidane ya aike da sakon fatan samun sauki ga dan wasan inda ya yi fatan warkewarsa don ya samu damar fafatawa a wasan na Ranar 6 ga watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.