Isa ga babban shafi
Wasanni

PSG ta bai wa Marsallie tazaran maki 10 a teburin Lig 1

Nasaran da PSG ta samu kan Troyes a gasar Lig 1 na Faransa, ya bata daman samu tazaran maki 10 tsakanin da Marsallie da ke mataki na 2 a teburi, yayin da Monaco ta sake yin kasa bayan rashin nasara a hannun Nantes.

'Yan wasan PSG
'Yan wasan PSG REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

PSG ta samu nasaran ci 2-0 a kwallayen da dan wasanta Neymar da Edison Cavani zuka zura.

Yayin da cin da Nantes ta yi wa Monaco minti 92 a tashi wasa ya tursasawa Monaco komawa mataki na 4 a teburi.

Marseille ta samu nasaran ci 3-0 kan Metz, wanda hakan ya bata daman haye matsayi na 2 sama lyon da ke na 3, wacce ta yi rashin nasara da ci 2-1 a hannu Lille.

Kwallayen da Florian Thauvin, Luiz Gustavo da Lucas Ocampos suka zara ya bai wa Mareille nasara a wasanni 9 ba tare da an ci ta ba, kazalika tana kusa da PSG.

A sauran wasanni kuma

Rennes ta samu nasara da ci 2-1 kan Angers

Nice ta yi wa Toulouse ci 2-1

Guingam da Montepellier sun tashi babu ci

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.