Isa ga babban shafi
wasanni

Dembele na Barcelona ba zai buga El-Clasico ba

Mai horar da Barcelona Ernesto Valverde ya ce, akwai yiwuwar dan wasansa Ousmane Dembele da ke fama da jinya, ba zai warke ba gabanin fafatawar da za a yi tsakanin Barcelona da Real Madrid da ake kira El Clasico a ranar 23 ga watan Disamba.

Ousmane Dembele na Barcelona
Ousmane Dembele na Barcelona REUTERS/Paul Hanna
Talla

Dembele da Barcelona ta siya a kan farashin Euro miliyan 105 daga Borussia Dortmund don maye gurbin Neymar a cikin watan Agusta, ya yi rauni ne a wasansu da Getafe a ranar 16 ga watan Satumba, kuma wasanni uku ya yi kungiyar.

Kocin ya nanata cewa, lallai raunin Dembele ya yi muni matuka kuma ya ce, ba za su yi kasadar sanya shi a wasa ba har sai ya samu cikakkiyar lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.