Isa ga babban shafi
Wasanni

IAAF ta ki janye haramcin shiga wasannin motsa jiki daga kan Rasha

Hukumar kula da wasannin motsa jiki ta duniya IAAF, ta ce ‘yan wasan Rasha zasu ci gaba da zama a karkashin haramcin shiga wasannin motsa jiki, saboda bata gamsu da matakan da gwamnatin kasar ke dauka ba, don dakile matsalar shan kwayoyin karin kuzari a tsakanin ‘yan wasanta ba.

Ministan wasanni na kasar Rasha, Vitaly Mutko, yayin tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Reuters, a birnin Moscow.
Ministan wasanni na kasar Rasha, Vitaly Mutko, yayin tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Reuters, a birnin Moscow. REUTERS/Maxim Zmeyev
Talla

Matakin na hukumar IAAF, ya zo ne gabannin taron da kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya IOC zai yi, musamman akan kasar ta Rasha, kan ko za’a bai wa ‘yan wasanta damar shga gasar Olympics na lokacin sanyi da kasar Korea ta Kudu zata karbi bakunci.

Sai dai a gefe guda, kwamitin ya ce ‘yan wasan da suka fito daga Rashan zasu iya fafatawa a gasar, amma da sharadin a matsayin ‘yan wasa da ke wakiltar kansu, ba kasarsu ba, idan aka tantance su.

A shekarar 2015, hukumar IAAF ta haramtawa Rasha shiga wasannin motsa jiki, bayan bullar wani rahoto da ya bankado cewa, da sanin gwamnatin kasar, wadanda ke wakiltarta a wasannin motsa jiki ke shan kwayoyin karin kuzari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.