Isa ga babban shafi
Wasanni

Monaco ta dauki Emenalo a matsayin daraktan wasanni

Kungiyar Monaco ta dauki Micheal Emenalo a matsayin sabon daraktan lura da wasanni.

Tsohon daraktan kungiyar Chelsea Michael Emenalo, wanda a yanzu ya koma kungiyar Monaco.
Tsohon daraktan kungiyar Chelsea Michael Emenalo, wanda a yanzu ya koma kungiyar Monaco. Reuters / John Sibley
Talla

Emenalo mai shekaru 52, ya kama sabon aikin bayan barin kungiyar Chelsea, inda ya rike matsayin daraktan tare da bai wa kungiyar gudunmawa matuka.

A lokacin da yake rike da daraktan wasannin Chelsea, kungiyar ta lashe kofunan Premier 3, kofunan FA 3, kofin Europa League da kuma kofin zakarun nahiyar Turai a shekarar 2012.

Zalika a karkashin, shugabancinsa ne na tsare-tsare da bada umarn, kungiyar Chelsea, ta sayo ‘yan wasanta da suka hada da Eden hazard, Thibaut Courtois da kuma Kante.

Micheal Emenalo, wanda tsohon dan wasan Najeriya ne, shi ne kuma ya tsarawa kungiyar Chelsea kafa makarantun horar da kwallon kafa a wasu sassan duniya, kuma daga cikinsu ne aka tattara matasan ‘yan wasan kungiyar da suka lashe kofin gasar matasa na kungiyoyi har sau biyu a jere, a shekarun 2015 da kuma 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.