Isa ga babban shafi
wasanni

"Manchester City ta wuce iyaka wajen murna"

Tsohon dan wasan Arsenal Ian Wright ya yi watsi da zargin cewa, Manchester City ta wuce iyaka wajen nuna murnar nasarar da ta samu kan Manchester United a karshen mako.

Nicolas Otamendi na Manchester City na murnar zura kwallo a ragar Manchester United a karshe mako
Nicolas Otamendi na Manchester City na murnar zura kwallo a ragar Manchester United a karshe mako Darren Staples/Reuters
Talla

Mutane na caccakar kungiyar saboda abin da suka kira rashin nuna aji wajen nuna murnar nasrar doke abokiyar hamayyarta

Amma cewar Wright, ya kamata a yi la’akari cewa, ‘yan wasan na Manchester City sun kafa tarihi ne, in da suka yi wasanni 14 a jere ba tare da an doke su ba.

Kazalika Wright na ganin cewa, ‘yar hatsaniyar da aka samu bayan kammala fafatawar ba ta da wani tasiri.

An dai jefi kocin Manchester United Jose Mourinho da madara bayan ya nuna adawa da bikin murnar.

Manchester City mai jan ragama a teburin firimiya ta Ingila ta samu nasarar ne da ci 2-1, in da kuma ta bai wa Manchester United tazarar maki 11.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.