Chelsea za ta kece raini da Barcelona
An hada ƙungiyoyi da za su kara a zagayen rukunin 16 na gasar zakarun nahiyar Turai inda Chelsea za su kece raini da Barcelona.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ƙungiyar Chelsea ta fi samun nasara a kan Barcelona cikin karawa 12 da ƙungiyoyin biyu suka yi a baya, inda ta doke Barcelona sau 4, yayin da Barcelona ta doke Chelsea sau 3.
A ranar Litini ne aka hada ƙungiyoyin
Sauran wasannin da za a kara su ne:
Basel da Manchester City
Bayern Munich da Besiktas
Juventus da Tottenham
Porto da Liverpool
Real Madrid da PSG
Sevilla da Manchester United
Shaktar Donetsk da Roma
Za a buga wasannin karo na farko ne a ranakun 13 da 14 na watan Maris, 2017.
Ƙungiyoyi biyar ne daga Burtaniya suka samu nasarar zuwa zagayen na 16 a gasar ta zakarun Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu