Isa ga babban shafi
wasanni

Burinmu na lashe kofi ya kawo karshe- Mourinho

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya bayyana cewa, ga alama burinsu na daukan kofin Firimiya a wannan kakar ya kawo karshe saboda yadda alkalin wasa Michael Oliver ya ki ba su bugun fanariti a fafatawar da Manchester City ta casa su da ci 2-1 a jiya Lahadi.

Kocin Manchester United, Jose Mourinho
Kocin Manchester United, Jose Mourinho Reuters/Jason Cairnduff
Talla

A cewar Mourinho alkalin wasan ya tafka babban kuskure a minti na 79, lokacin da Ander Herrera ya fadi bayan Otamendi ya kai ma sa hari a kusa da gidan golan Manchester City.

Mourinho ya ce, kamata ya yi su tashi 2-2 amma ya zargi alkalin wasan da rashin yi mu su adalci.

Yanzu haka Manchester City ta zamo kungiyar kwallon kafa ta farko a Ingila da ta lashe wasanni 14 a jere kuma a cikin kaka guda a Firimiya, yayin da ta ke jan ragama da maki 46 a teburin gasar, in da ta bai wa Manchester United tazarar maki 11.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.