wasanni
Ga alama Neymar na cikin damuwa
Rahotanni na cewa, Neyma na PSG ya yi tafiyar gaggawa zuwa kasarsa ta asali wato Brazil bayan ya samu mummunan labari game da danginsa kamar yadda gidan rediyan RMC na Faransa ya rawaaito.
Wallafawa ranar:
Talla
Gidan rediyon wanda ke watsa zallan labaran wasanni ya ce, cikin daren da ya gabata ne Neymar ya yi balaguron da bai kintsa ma sa ba.
Neymar na yawan aika sakonni a shafuka sada zumunta amma masu bibiyansa a shafinsa sun lura cewa, tun a ranar juma’ar da ta gabata, raban da ya aike da wani sako a dandalin shafukan sada zumunta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu