Isa ga babban shafi
kwallon kafa

PSG ta sake danewa saman teburin gasar French Ligue

Paris Saint Germain ta sake danewa saman teburin gasar Faransa, wato French Ligue a jiya, bayan dan wasanta Zlatan Ibrahimavic ya zira kwallonsa ta 19 a wannan kakar wasa a lokacin da suka doke Bordeaux da ci 1-0. Ya kuma zira kwallo ne a cikin mintin biyu kamin a je hutun rabin lokaci.  

Zlatan Ibrahimovic a lokacin da París Saint Germain, ke karawa da Saint Etienne.
Zlatan Ibrahimovic a lokacin da París Saint Germain, ke karawa da Saint Etienne.
Talla

A wancan karshen makon da ya gabata, Lyon ta shure PSG daga saman teburin bayan ita PSG din ta tashi babu ci kodaya a wasan da ta buga da Ajjacio.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga a gasar na nuna cewa Lille ta sha mamaya a gidanta bayan Nice ta doke da ci 2-0, kana Bastia itama ta sha mamaya a gida a lokacin da Rennes ta lallasa ta 2-0.

Marseille kuma ta doke Montellier da ci 3-2, a dai dai lokacin da Brest ta sha kayi a hanun Saint- Etienne da 1-0.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.