Isa ga babban shafi
Euro 2012

Euro 2012: Holland da Denmark sun fice, Portugal ta sha da kyar

Kasar Holland da Denmark sun fice gasar Cin kofin Turai, bayan sun sha kashi hannun Portugal da Jamus a Rukuninsu na B da ake kira rukunin Mutuwa. Portugal dai ta sha da kyar ne bayan ta doke Holland ci 2-1, kasar Jamus ce kuma ta jagoranci rukunin na mutuwa inda ta lallasa Denmark ci 2-1.

Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo a tsakiya tare da abokan wasan shi Ruben Micael da Fabio Coentrao sun murnar lashe wasansu da Holland a gasar kofin Turai a filin wasa na Kharkiv
Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo a tsakiya tare da abokan wasan shi Ruben Micael da Fabio Coentrao sun murnar lashe wasansu da Holland a gasar kofin Turai a filin wasa na Kharkiv
Talla

Wasannin da aka gudanar a jiya dai an yi kare-jini-biri-jini ne domin dukkanin kasashen suna iya tsallakewa zagayen Quarter final.

Cristiano Renaldo dai ya amsa kalubalen da ake masa, domin shi ne ya zira wa Portugal kwallayenta biyu a ragar Holland.

A wasan Portugal da Denmark ne ‘Yan kallo suka yayata Messi a filin wasa domin kunyata Ronaldo wanda tun fara gasar Turai sai a jiya Lahadi ne ya zira kwallo a raga.

Yanzu haka dai a ranar Alhamis ne Jamus zata kara da kasar Girka a zagayen Quarter final bayan Girka ta zo matsayi na biyu a rukunin A, Sai kuma Portugal ta fafata da Jamuhuriyyar Czech.

Wasan Girka da Jamus wasa ne da za’a kwashi ‘yan kallo saboda kazamar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu saboda rikicin tattalin arzikin kasashen Turai.

Al’ummar Girka dai suna adawa da Jamus, musamman shugaban gwamnatin kasar, Angela Merkel da ke matsin lamba wajen ganin Girka ta aiwatar da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati, matakin da al’ummar kasar ke adawa da shi.

Don haka wasa tsakanin Girka da Jamus za’a banbance gari ne da tsakuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.