Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Madrid da Juventus sun sha kashi, Bayern da United da Barca sun haska

Manchester City ta rike Chelsea a Stanford Bridge ba tare da zira kwallo a raga ba inda aka tashi wasan babu ci duk da a wasan ne da sabon kocin Chelsea Rafael Benitez ya fara haskawa. Masoya Chelsea sun ta yayata kalaman kyamatar Benitez da aka dauka matsayin koci bayan sallamar Di Matteo.

Kocin Real Madrid  Jose Mourinho yana lallashin Sergio Ramos bayan sun sha kashi ci 1-0 a gidan Real Betis
Kocin Real Madrid Jose Mourinho yana lallashin Sergio Ramos bayan sun sha kashi ci 1-0 a gidan Real Betis REUTERS/Marcelo del Pozo
Talla

Yanzu haka dai kungiyar Chelsea ita ce a matsayi na Hudu a Teburin Premier, tazajar maki daya tsakaninta da West Brom Albion da ke a matsayi na uku.

Manchester United ce a saman Teburin Premier wace ta doke QPR ci 3-1. Manchester City ce a matsayi na biyu bayan an tashi wasa babu ci tsakaninta da Chelsea.

Wasa tsakanin Swansea da Liverpool kuma an tashi ne babu ci kamar yadda aka tashi wasa babu ci tsakanin Aston Villa da Arsenal.

Spain

A La liga, Lionel Messi ya zira kwallaye biyu a raga wanda ya taimakawa Barcelona doke Levente ci 4-0. Tazarar maki uku ne dai har yanzu Barcelona taba Atletico Madrid da ke take mata baya a Teburin La liga

Yanzu haka dai a bana Messi ya zira kwallaye 82, kuma saura kwallaye uku kacal Messi ya kamo Mueller na Jamus wanda ya zira kallaye 85 a kakar wasan shekarar 1972.

Kungiyar Real Madrid kuma ta sha kashi ne ci 1-0 a gidan Real Betis, kuma yanzu tazarar maki 11 ke nan Barcelona ta ba Real Madrid a teburin La liga. Atletico Madrid kuma ta ba Real Madrid tazarar maki 8 ne bayan Atletico ta lallasa Sevilla ci 4-0.

Messi ne dai ke da yawan kwallaye 19 a Raga, yayin da kuma Cristiano Ronaldo ke bi masa da kwallaye 12. Sai Rademel Falcao a matsayi na uku da kwallaye 11.

Jamus

A Jamus Bayern Munich ce ke jagorancin Teburin Bundesliga da maki 9 Bayan ta lallasa Hanover ci 5-0.

A karshen makon mai zuwa ne dai za’a yi karon batta tsakanin Bayern Munich da Borussia Dortmund bayan Bayern ta kece raini da Friegburg a ranar Laraba.

Italiya

A Seria A, AC Milan ta samu sa’ar Juventus ci 1-0. Robinho ne dai ya zirawa AC Milan kwallonta a ragar Juve amma a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Juventus ce dai ke jagorancin Teburin Seria A amma AC Milan tana matsayi na 9 ne a teburin gasar.

Inter Milan da ke bi ma Juve a Tebur a yau Litinin ne za ta kece raini da Parma yayin da kuma Cagliari za ta kara da Napoli.

Faransa

A Faransa, Marseille tana jayayyar Tebur ne da PSG inda dukkaninsu ke da maki 26, bayan Marseille ta doke Lille ci 1-0, PSG kuma ta lallasa Troyes ci 4-0.

Kungiyar Toulouse ta lallasa Lyon ci 3-0. Bordeaux kuma ta sha kashi ne ci daya mai ban haushi hannun Montpellier.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.