Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

City da Lyon sun dare Tebur, Barca da Madrid sun haska

Kungiyar Lyon ta dare Teburin French League a Faransa bayan lallasa Reims ci 3-0. Bordeaux ce ke bi ma Lyon a matsayi na biyu da tazarar maki daya a tebur, bayan Bordeaux ta doke Marseille ci 1-0.

Roberto Mancini kocin Manchester City
Roberto Mancini kocin Manchester City
Talla

Yanzu kuma tazarar maki Biyu ne Lyon taba PSG da ke matsayi na uku bayan PSG ta sha kashi ci 2-1 a hannun Rennes.

Ingila

A Ingila, kashin da Manchester da Chelsea suka sha a karshen mako ya ba Manchester City damar darewa teburin Premier bayan ta lallasa Aston Villa ci 5-0.

Manchester United dai ta sha kashi ne hannun Norwich City ci 1-0, yayin da kuma chelsea ta fuskanci barazana karo na hudu ana samun galabarta bayan ta sha kashi hannun West Bromwich Albion. Ci 2-1.

Arsenal kuma ta doke makwabiciyarta Tottenham ci 5-2. Adebayor yana cikin wadanda suka zira wa Tottenham kwallo a raga amma alkalin wasa ya ba shi jan kati bayan ya noshe Santi Kazorla.

Mertesacker da Lukas Podolski da Olivier Giroud da Cazorla da Theo Walcott su ne suka zirawa Arsene Wengar kwallaye a raga.

Spain

A Spain, Atletico Madrid ce ke ci gaba da Matsin lamba ga Barcelona a teburin La liga bayan a daren jiya Lahadi Atletico Madrid din ta kaci kanta hannun Granada ci 1-0.

Tazarar maki uku ne dai Barcelona ta ba Atletico Madrid, maki 8 kuma tsakaninta da Real Madrid.

A karshen mako Barcelona ta doke Real Zaragoza ne ci 3-1. A wasan ne kuma Messi ya zira kwallaye biyu. Kazalika a wasan ne dan wasan Kamaru Alex Song ya zira kwallon farko a Barcelona.

Real Madrid kuma ta lallasa Athletic Bilbao ne ci 5-1. Duk da wadannan ruwan kawallayen, Cristiano Ronaldo bai samu damar zira kwallo ba. Ramos da Benzema da Ozil da Khedira su ne dai suka zira wa Madrid kwallayenta a raga.

Italiya.

A Seria A Cagliari ta rike Inter Milan ci 2-2 a San Siro kamar yadda aka tashi wasa ci 2-2 tsakanin AC Milan da Napoli yayin da kuma aka tashi wasa babu ci tsakanin Juvenstus da Lazio.

Juventus ce dai a saman Teburin Seria A tazarar maki 4 tsakaninta da Inter Milan.

Jamus

A Bunsedelia kuma a kasar Jamus Bayern Munich Ke jagorancin teburin gasar da tazarar maki 8 bayan Schalke 04 ta sha kashi 2-0 a hannun Leverkusen.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.