Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Inter ta sha kashi, Messi ya sha gaban Pele a tarihin zira kwallo a raga

Dan wasan Barcelona Lionel Messi ya sha gaban mazan jiya, Pele na brazil a duniyar zira kwallo a raga bayan ya zira kwallaye biyu da Barcelona ta doke Mallorca ci 4-2. Messi yanzu yana neman ya kamo kafar Muller ne wanda ya zira kwallaye 85 a kakar wasa a shekarar 1972.

Dan wasan Barcelona Lionel Messi yana tabewa da abokan wasan shi bayan ya zira kwallo a ragar Depotivo.
Dan wasan Barcelona Lionel Messi yana tabewa da abokan wasan shi bayan ya zira kwallo a ragar Depotivo. REUTERS/Miguel Vidal
Talla

Yanzu kwallaye 76 ne Messi ya zira a raga a bana wanda ya bashi damar shan gaban Pele na Brazil wanda ya zira kwallaye 75 a shekarar 1958 da kungiyar Santos.

A daya bangaren kuma Matashin dan wasa Alvaro Morata shi ne ya kwaci Madrid wanda ya zira kwallo ta biyu a hannun Levente a haskawar shi ta farko a tawagar Mourinho.

Cristiano Ronaldo ne dai ya fara zira kwallo a raga kafin Angel Rodriguez ya barke kwallo. amma Xavi Alonso ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Har yanzu dai Barcelona ce saman Teburin La liga, tazarar maki uku tsakaninta da Atletico Madrid. Real Madrid ce a matsayi na uku

Ingila

A Ingila John Terry ya zira kwallo a ragar Liverpool amma ya fice wasan saboda rauni. Kocin Chelsea Roberto Di Matteo yace za’a dauki hoton gwiwar John Terry domin diba lafiyar shi bayan dan wasan ya samu rauni a wasan farko da ya yi haskawar farko da Liverpool bayan dakatar da shi.

John Terry shi ne ya zira wa Chelsea kwallo a ragar Liverpool ana minti 20 da fara wasa, kuma wannan ne kwallon shi ta 50 a rayuwar shi a Chelsea amma kuma ana minti 39 da wasa ne John Terry ya yi wata taho mu gama da Suarez wanda ya sa aka fice da shi daga filin wasa.

Suarez ne dai ya barke kwallon da John Terry ya zira wanda ya mayar da Chelsea matsayi na uku a Teburin Premier. Manchester City ce yanzu a matsayi na biyu bayan doke Tottenham.

Manchester United ce dai a saman Teburin Premier da maki 27 tazarar maki biyu tsakaninta da City, maki uku kuma tsakaninta da Chelsea. Bayan United din tasha da kyar hannun Aston Villa ci 3-2.

Wasa tsakanin Arsenal da Fulham kuma an tashi ne ci 3-3, Giroud da Podolski sune suka zirawa Arsenal kwallayenta a raga yayin da Berbatov ya zira kwallaye biyu a ragar Arsenal.

Italiya

A Seria kuma Inter Milan ba ta sha da dadi ba domin tasha kashi a hannun Atlanta, ci 3-1 wanda hakan kwarin gwiwa ne ga Juventus da ke saman Teburin gasar.

Kazalika Roma ta sha kashi a hannun Lazio kamar yadda aka kwashi kallo tsakanin Fiorentina da AC Milan, Napoli kuma ta doke Genoa ne ci 4-2.

A Filin wasa na San Siro AC Milan ta sha kashi ne a hannun Fiorentina. Ci 3-1 kuma a wasan ne Alexandre Pato ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron

Faransa

Paris Saint-Germain ta yi kunne doki ne tsakaninta da Montpellier mai rike da kofin gasar. Kuma Dukkanin kungiyoyin biyu alkalin wasa ya rage yawan ‘Yan wasansu zuwa mutane goma goma.

Haka kuma wasa tsakananin Marseille da Nice an tashi ne ci -2-2.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.