Isa ga babban shafi
Olympics

'Yan Sandan Faransa na zanga-zangar neman karin alawus

‘Yan sanda a Faransa na gudanar da zanga-zangar tilasta wa gwamnati yi musu karin alawus don samun kwarin gwiwar aikin tabbatar da doka da oda a lokacin gasar Olympics.

'Yan Sandan Faransa yayin zanga-zanga a birnin Paris
'Yan Sandan Faransa yayin zanga-zanga a birnin Paris AFP - DIMITAR DILKOFF
Talla

Jami’an tsaron da aka dora musu yin aiki na musamman a lokacin gasar ta Olympics na ganin sun cancanci samun karin kudi fiye da takwarorinsu da ba za su yi wani aiki lokacin gasar ba.

La’akari da zaman doya da manja da gwamnati ke yi da kungiyoyin kwadago masu bukatar a yi wa ma’aikata karin albashi, ya sanya gwamnatin kasar jan kafa wajen amsa bukatar ‘yan sandan.

Tuni dai sauran sassan kungiyoyin ‘yan sanda suka bukaci mambobinsu da su ma su kwarara kan tituna don marawa wannan zanga-zanga baya, da nufin tilasta wa gwamnati amsa bukatarsu.

‘Yan sandan sun ayyana shirinsu na gudanar da zanga-zangar dare da rana har sai gwamnati ta amince da biyansu karin alawus na kimanin Yuro dubu biyu.

Yayin da Faransa ke fuskantar barazanar tsaro da kuma irin tarin jama’ar da za su hallara lokacin gasar, ana ganin aiki ne zai karu kan ‘yan sandan yayin da za su rasa cin moriyar hutun aiki da makarantu da za a bayar a wannan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.