Isa ga babban shafi
SHAIDAR-RIGAKAFI

Faransawa dubu 250 suka shiga zanga zangar adawa da gwamnati

Akalla mutane dubu 250 suka shiga zanga zanga yau a kasar Faransa domin nuna rashin amincewar su da umurnin shugaba Emmanuel Macron na tilastawa jama’ar kasar nuna takardar shaidar karbar allurar rigakafin cutar korona kafin basu damar shiga gidajen sayar da abinci ko kuma tafiya a jiragen sama da kasa.

Masu zanga zanga a birnin Nantes
Masu zanga zanga a birnin Nantes AFP - SEBASTIEN SALOM-GOMIS
Talla

Umurnin shugaban yace ya zama dole ko wane dan kasa ya gabatar da takardar karbar allurar rigakafin sau biyu ko kuma shaidar cewar baya dauke da cutar kafin shiga wadannan wurare daga ranar litinin mai zuwa.

Shugaba Macron dake fuskantar zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa ya gabatar da dokar ne domin karfafawa jama’ar kasar damar karbar allurar rigakafin domin kawar da cutar korona daga kasar, amma kuma masu adawa da ita na ci gaba da gudanar da zanga zanga saboda abinda suka kira take musu hakkokin su.

Masu zanga zanga a Paris
Masu zanga zanga a Paris AFP - STEPHANE DE SAKUTIN

Ma’aikatar cikin gida tace mutane dubu 237 suka shiga zanga zangar a sassan kasar Faransa, yayin da dubu 17 suka shiga wadda akayi a birnin Paris, abinda ya zarce dubu 240 da aka gani a makon jiya.

Wadanda suka shiga zanga zangar a Paris sun yi ta ihu suna bayyana ‘Yanci da kuma ‘Macron bama bukatar takardar shaidar ka’.

Rahotanni sun ce akalla mutane dubu 37 suka shiga zanga zangar a Yankin Cote d’Azur dake gabar tekun Meditereniya da biranen Toulon da Nice da Marseille inda suke cewa takardar shaidar kasha ‘yancin jama’a ne.

Ranar litinin ake saran sabuwar dokar ta fara aiki, kuma tuni kotun Fasalta kundin tsarin mulki ta amince da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.