Masu zanga zanga a Faransa na ci gaba da kona motoci da sauran dukiyoyi a Paris
An ci gaba da Zanga-zangar adawa da kisan wani matashi da wani dan sanda ya yi a Faransa a dare na 3 a jere a jiya Alhamis, inda aka kona motoci tare da lalata gine-gine, kuma ‘yan sanda suka kama daruruwan mutane a fadin kasar.
Wallafawa ranar:
Tarzomar ta cikin dare na zuwa ne bayan wani tattaki da aka yi tun da farko a ranar Alhamis don tunawa da matashi Nahel, mai shekaru 17 wanda mutuwarsa ta farfado da dadaddiyar korafin da ake da ita a kan yadda ake gama aikin dan sanda da nuna wariyar launin fata a yankunan marasa galihu da biranen Faransa masu kunshe da kabilu mabanbanta
Tun da farko wata sanarwa daga mahukunta ta nuna cewa ana sa ran samun tarzoma a cikin dare, lamarin da ya sa suka jibge ‘yan sanda da jandarmomi har dubu 40 a sassan kasar.
Akalla birane 3 a kewayen birnin Paris sun sanya dokar takaita zirga-zirga, baya ga haramta taruka a bainar jama’a, inda ake iya ganin jirage masu saukar ungulu da masu sarrafa kansu suna shawagi a biranen Lille da Tourcoing a arewacin kasar.
Duk da dimbin jami’an tsaro da aka baza, an samu rahotannin tarzoma da barna a yankuna da dama, kuma da misalin karfe 3 na asubahin Juma’ar nan, tawagar ministan cikin gidan kasar Gerald Darmanin ta ce an kama akalla mutane 421 a cikin daren.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu