Isa ga babban shafi

'Yan sanda sun kama mutane 150 yayin zanga-zangar kisan wani matashi a Faransa

Masu zanga zanga a Faransa sun fusata, biyo bayan kisan gillar da ‘yan sandan kasar suka yi wa wani matashi dan shekaru 17 a birnin Paris, lamarin da ya haifar da rikicin da tuni ya yadu zuwa sassan biranen kasar, duk da karfafa matakan tsaro da kuma kiran da Shugaban Kasar yayi a kwantar da hankula. 

Jami'an 'yan sandan Faransa lokacin da suke kama wasu daga cikin masu zanga-zangar.
Jami'an 'yan sandan Faransa lokacin da suke kama wasu daga cikin masu zanga-zangar. © Michel Spingler / AP
Talla

Hoton bidiyon da ya nuna yadda jami’an suka kashe Nael a ranar Talata, lokacin da suke cikin aikin bincike, ya tayar da hankulan alummar Kasar, ya kuma haddasa rikici tsakanin matasa da jami’an ‘yan sanda a birane da dama na kasar. 

Tun a daren Talatar da ta gabata ne rikicin farko ya barke a ciki da wajen garin Nanterre dake birnin Paris inda aka kashe Nael, wanda a dalilin faruwar lamarin gwamnati ta jibge jami’an ‘yan sanda dubu 2 a yankin, domin kwantar da tarzomar. Sai dai duk da haka rikicin ya ci gaba wayewar garin ranar Alhamis. 

Kakakin ‘yan sandan kasar ya ce Jami’an ‘yan sanda da ‘yan kwana-kwana sun yi duk mai yiwuwa wajen kwantar da hankulan fusatattun mutanen tare da kashe gobarar da ta tashi a mabanbantan wurare, wanda yayi sanadiyar lalata makarantu, da ofishin ‘yan sanda da wani dakin taro hade da wasu gine gine. 

A Alhamis din nan rundunar ‘yan sandan Faransa ta kuma sanar da samun harbe harbe da barkewar rikice rikice cikin dare a birane da dama, daga birnin Toulouse dake kudancin kasar da kuma Lille dake arewacin Kasar, ko da yake rikicin ya soma ne daga  garin Nanterre da sauran sassan Paris.  

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya gudanar da taron gaggawa da bangaren tsaron Kasar game da rikicin, yayin da a cewar kakakin ‘yan sandan kasar ya zuwa wannan lokaci sun cafke akalla mutane 150 a rikicin, fiye da rabin adadin su a birnin Paris. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.