Isa ga babban shafi

Faransa ta ware euro dubu 600 don bunkasa Faransanci a Najeriya

Gwamnatin Faransa ta sanar da aniyarta ta ware euro dubu 600 domin bunkasa harshen Faransanci a Najeriya tare da fatan ya zama na biyu a jerin harsunan da ake magana da su a hukumance a fadin kasar.

Wata ziyara da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya taba kawo wa Najeriya.
Wata ziyara da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya taba kawo wa Najeriya. Reuters/Afolabi Sotunde
Talla

A tashin farko, gwamnatin Faransa za ta yi amfani da wadannan kudade wajen kara ilmantar da malaman da ke koyar da harshen Faransanci a  makarantun sakandare na Najeriya, yayin da kuma za ta sayo tarin littattafan koyon yaran don rarraba wa dalibai.

Kazalika gwamnatin ta Faransa za ta dauki nauyin wasu daga cikin malaman na Faransanci domin horas da su a can Faransa kafin su dawo Najeriya don ci gaba da aikinsu na koyarwa.

A yayin zantawarta da Sashen Hausa na RFI, jakadiyar Faransa a Najeriya, Emmanuelle Blatmann ta ce, jihohi biyar na Najeriya ne za su fara cin gajiyar wannan sabon shirin.

Kazalika za mu sayi kimanin littattafan karatu dubu 5 ga daliban da ke tsakanin shekara 11 zuwa 15 na haihuwa, sannan za a shirya horaswa ta musamman a Najeriya tare da aike wa da malamai zuwa Faransa domin samun karin horon tsawon makwanni biyu zuwa uku.Za kuma mu sayi kwamfutoci da majigi ga makarantu. Ina zaton kasafin kudin a tsuke yake, dalilin da ya sa muke son farawa da jihohi biyar kenan, amma muna fatan kara yawan kudin bayan mun samu sakamako mai kyau”

Ku latsa alamar sauti da ke kasa domin sauraren muryar Jakadiyar Faransar a Najeriya kan wannan shirin.

00:38

Muryar Jakadiyar Faransa a Najeriya

Burin shirin ba wai takaita magana da harshen Faransanci a tsakanin makarantu ba ne kawai, har ma da wuraren tarukan jama’a a Najeriya  gami da aiki tare da kafafen da ke yada labarai cikin wannan harshe a kasar.

Jihohin da za su fara cin gajiyar shirin sun hada da Lagos da Abuja da Filato da Oyo da Enugu.

Za kuma a samar da wasu shirye-shirye na ilmantarwa da za su bai wa manya da kananan yara damar koyon harshen Faransanci cikin sauki.

Akwai dai dimbin makarantu a Najeriya da suka hada da jami’o’i da ke koyar da harshen Faransanci a yanzu haka, yaran da tun da jimawa gwamnatin kasar ke da burin mayar da shi a matsayin na biyu bayan turancin Ingilishi da aka fi magana da shi a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.