Isa ga babban shafi

Ba zan yadda na tafka kuskuren da Antony Joshua yayi ba-Tyson Fury

Nan kuma fitaccen dan wasan dambe Tyson Fury ya jaddada cewa ko kusa ba zai yadda ya yi makamancin kuskuren da wasa Antony Joshuwa ya yi a wasan sa da Andy Ruiz, a dambacewar da zai yi da Francis Ngannou ba.

Dan wasa Tyson Fury
Dan wasa Tyson Fury AFP/File
Talla

Tyson yace shi wasa ya je yi, ba kuma zai yadda a shigar da shi cikin siyasar da ta daibaibaye wasanni ba, yana mai cewa wannan shine gagarumin kuskuren da Antony Joshua ya tafka har ta kai shi ga rashin nasara.

Dan wasan Fury ya kuma ci gaba da cewa yaddda ‘yan wasan dambe ke yiwa kananan ‘yan wasa kallon raini, shine babban dalilin da ke sanya su shan kunya yayin karawa, inda ya ce zai dauki Ngannou a matsayin babban dan wasa, don haka zai jigbe shi ne tamkar yana dukan fitaccen dan was aba tare da tausayi ba.

Dan wasan ya buga misali da yadda Anthony Joshua ya rika kalamai irin na raini a lokacin da yake shirin buga wasa da Andy Ruiz a birnin New York, inda ya ce wannan na cikin dalilin da ya hana shi atisaye, a ganin sa ba yadda Andy zai yi da shi, sai ga shi ya bashi mamaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.