Isa ga babban shafi

McGregor na fuskantar tuhuma kan zargin cin zarafin mata

Masu shigar da kara a Amurka sun fara tuhumar fitacccen dan damben UFC Conor McGregor da zargin cin zarafin wata mata a lokacin da ake wasan karshe na gasar kwallon Kwando ta NBA birnin Miamin Amurka cikin watan nan.

Fitaccen dan damben UFC Conor McGregor.
Fitaccen dan damben UFC Conor McGregor. © Getty Images via AFP - STEVE MARCUS
Talla

Wata wasika da aka aikewa McGregor ta yi zargin cewa dan damben ya bi wata mata har makewayi a cibiyar Kaseya tare da cin zarafinta lokacin da ake wasan na karshe, ko da ya ke lauyansa ya musanta zargin.

Lauyan na McGregor ya ce baza su amince da bata sunan dan damben ba.

Tuni dai Ofishin ‘yan sanda na Miami ya bude bincike kan zargin da ake yiwa fitaccen dan damban yayinda kwamitin gudanarwa na UFC ya bayyana cewa yana sane da zargin kuma ya fara bincike don tattara hujjoji.

Lauyar matashiyar da ke zargin McGregor da cin zarafinta Ms Ariel Mitchell ta bayyana cewa matashiyar na tsaka da kallon wasan karshe na ranar 9 ga watan nan ne lamarin ya faru.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.