Isa ga babban shafi

Joshua ya bayyana sha'awar zama jarumin fim idan ya daina dambe

Tsohon zakaran damben boxing ajin masu nauyi sau biyu, Anthony Joshua na Birtaniya dan asalin Najeriya, ya bayyana cewa zai so ya shiga wasan kwaikwayo da zarar ya daina wasan dambe.

Anthony Joshua
Anthony Joshua © Reuters/Andrew Couldridge
Talla

Joshua ya bayyana haka ne yayin hira da wata mujalla ta kasa da kasa mai suna GQ.

A cewar Joshua, wasan damben boxing ya bude masa kofofi da dama musamman bayan da ya lashe lambar zinare a gasar ajin masu nauyi a gasar Olympics ta 2021 a birnin Landan.

Dan damben mai shekaru 33 ya bayyana irin son da yake yi wa fina-finai a kasar Amurka.

Sau biyu ne dai Joshuwa ya sha dukan tsiya a hannun Oleksander Usyk na Ukraine, abinda ya sanya shi rasa kambinsa na WBO, IBF, WBC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.